Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Nijeriya Sun Kashe Barayin Man Fetur Goma Sha Biyu


Hukumomin Nijeriya sun ce sojoji sun kashe mutane 12 dake satar mai daga bututun danyen mai a Jihar Delta a kudancin kasar. Wannan lamari ya faru tun ranar asabar a kusa da Oghara.

Jami’ai suka ce sojojin dake aikin sintiri sun hango wasu mutane 20 da ake kyautata zaton barayi ne a jikin wani bututun mai na kamfanin Pan Ocean Oil. Daga nan aka fara musanyar wuta da bindigogi a tsakanin mutanen da sojoji.

An kashe 12 daga cikin mutanen, uku suka ji rauni, aka kuma kama sauran biyar da suka rage.

Mutanen suna dauke da injuna na sace mai daga bututu da kuma tankokin mai guda hudu a lokacin da aka hango su.

XS
SM
MD
LG