Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun bayar Da Umurnin Kwashe Mutane Daga Wasu Unguwannin Birnin Oklahoma


Wutar daji ta barke a wurare da dama a yankin kudu maso yammacin Amurka, tana kuma kara ruruwa a saboda iska mai karfi dake kadawa da kuma zafi da rashin ruwan sama a yankin.

Hukumomi sun bayar da umurnin a kwashe mutane daga wasu unguwannin birnin Oklahoma, inda gidaje masu yawa suka kone kurmus. Wasu mutanen ma an ba su ’yan mintoci kadan ne kawai da su kwashi abinda zasu iya kwasa a cikin gidajensu su fice.

Jami’ai sun ce a yanzu dai wutar ba ta yin barazana ga tsakiyar birnin Oklahoma, inda daruruwan dubban mutane suke zaune ko suke aiki. Gwamna Brad Henry na Jihar Oklahoma ya ce ya nemi shugaba Bush da ya gaggauta kai musu taimako daga gwamnatin tarayya.

Wutar dajin ta kuma yi barazana ga gidajen jama’a da yawa a jihohin Texas da New Mexico a jiya lahadi.

Tun daga makon jiya, wutar ta kona dubban kadada na daji a jihohin New Mexico, Oklahoma da Texas. Masana yanayi sun yi hasashen cewa iskar dake kadawa zata ragu, amma kuma za a ci gaba da fuskantar karancin ruwan sama.

XS
SM
MD
LG