Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MAHAJJATA SUN HALAKA A WAJEN JIFA


Hukumomi a Saudi Arabia da kuma shdun gani da ido sunce mutane da dama sun halaka a wajen jifan Shedan a ranar ta karshe na aikin Hajjin bana. Labarin farko yace mutane 57 ne suka rasa rayukansu, amma bayan da 'yan aikin ceto suka ci gaba da kwaso gawarwaki, an sami wadanda suka kwanta damar sun wuce dari 3 da 45. Mahajjatan sun yi ta faduwa ana takasu a wajen cunkoson mutane fiye da dubu sittin a wajen jifar Shedan din. A bana hukumomin Saudiyyar sun sauya fasalin yadda ake bi aje wajen jifar domin a magance mace-macen da ake samu alokacin jifar. A makon jiya ma sama da mutane 76 ne suka rasa rayukansa a lokacin da wani ginin Otel ya rushe kan mutane. Ya zuwa wannan lokaci dai bamu san Alhazan wadanne kasashe ne suka rasa rayukansu ba.

XS
SM
MD
LG