Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kuri'ar raba Garda akan tsarin mulkin kasar Congo ta goyi baya a gyara kundin


Humumar Zaben kasar Demokradiyyar kasar Congo, tace akasarin 'yan kasar da suka kada kuri'r raba gardama akan gyaran tsarin mulkin kasar sun amince akan a sake kundin tsarin mulkin. A wata sanarwar sakamakon kuri'ar da hukumar ta bayar jiya Laraba, tace kashi Tamanin da Hudu daga cikin 100 na wadanda suka kada kuri'ar, sun nuna amincewa akan a sake tsarin mulkin, abinda ake gani a matsayin matakin farko na bin tafarkin dimokradiyyar kasar. A wajejen watan Yuni na bana ne ake sa rai za'ayi babban zabe, abinda zai kawo karshen kazamin tashin hankalin da akayi a kasar wanda yaci rayukan 'yan kasar da dama.

XS
SM
MD
LG