Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wanda ya nemi kashe Papa Roma, ya fita daga  tsari


An saki dan bindigan nan da ya yi yunkurin kashe Marigayi Papa Roma John Paul na II a shekara ta 1981. Mutumin dan kasar Turkiya ne. A yau aka sake shi, kuma lokacin da zai fito daga gidan kaso, 'yan ra'ayin kishin kasa na kasar Turkiya sunyi kwamba a kofar shiga gidan kurkukun suna ta murna a lokacin da zai fita daga gidan kurkukun a birnin Istambul. Yana fitowa sai suka barke da ihu na murnar fitowarsa. Mutumin mai suna Mehmet Ali Agca, an daukeshi nan take zuwa wani waje da ake diban sabbin kuratan soja. Ya share shekaru 20 yana tsare a gidan sarka.

XS
SM
MD
LG