Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Dake Yin Garkuwa Da Ma'aikatan Mai Hudu A Nijeriya Sun Bayar Da Wa'adin Kwanaki Biyu


'Yan tawayen Nijeriya dake yin garkuwa da ma'aikatan mai hudu 'yan kasashen waje, sun bayar da wa'adin kwanaki biyu, ko sa'o'i 48, da a biya musu bukatun da suka gabatar.

A cikin tattaunawa ta wayar tarho da sakonnin Email ga kamfanonin dillancin labarai, wata kungiyar dake kiran kanta "Kungiyar 'Yantar Da Yankin Niger Delta" ta ce tana son a mayar da ikon mallakin arzikin mai na yankin a hannun 'yan wannan yanki. Har ila yau ta bukaci kamfanin mai na Shell da ya biya diyyar dala miliyan dubu daya da dari biyar a saboda gurbata yankin. Ita kuma gwamnatin Nijeriya an bukace ta da ta sako wasu fursunoni uku, cikinsu har da wasu shugabannin kabilar Ijaw guda biyu.

Kungiyar ta yi barazanar zafafa hare-haren da take kaiwa kan cibiyoyin mai na Nijeriya idan har ba a biya mata bukatunta ba. A bayan sace ma'aikatan mai da aka yi a makon jiya, 'yan tawaye sun tarwatsa wani bututun mai na kamfanin Shell, suka kuma kai farmaki kan wata tashar tura mai mallakin kamfanin.

Gwamnatin Nijeriya ta tura wata tawagar soja ta musamman domin ta yi kokarin sako mutanen da aka kama ake garkuwa da su.

XS
SM
MD
LG