Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam na Kunar bakin wake ya kashe mutane 15 a birnin Bagadaza


Ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar Iraq, tace mutane 15 sun rasa rayukansu sannan 25 kuma sun ji mammunan rauni a lokacin da wasu bama bamai biyu suka tashi a tsakiyar birnin Bagadaza. Ma'aikatar tace wani dan kunar bakin wake ne yaje wata mashaya inda ke ciki da farar hula ya tarwatsa kansa, inda ya kashe mutane 12 a wannan rana ta Alhamis da rana tsaka. A wani gefen kuma wani Bam din ya kashe akallan mutan uku. A halin yanzu kuma jami'an gwamnatin kasar Iraq sun ce sun umurci sojojin Amirka akan su saki wasu mata fursunoni shidda daga cikin Takwas da ake rike da su. Duk da haka sunce wannan shikar batada alaka da rike 'yar jaridan nan ba Amirkiya da 'yan bindiga suka sace a makon jiya. Jiya Laraba da marece kuma 'Yan bindiga dadi sun kashe masu gadi su goma a sannan suka sace wani injiniya dan Afrika a lokacin da suka kai wata sumame kan tawagar jami'an tsaro na wani kamfani mai zaman kansa a birnin Bagadaza. Sace wannan injiniya yayi kacibis da lokacin da wadanda suka sace 'yar jaridannan Jill Carroll a suka yi barazanar zasu kashe ta. Tashar talbijin na Aljazeera ta nuna Caroll a wani hoton Bidiyo a ranar Talata ta na magana amma ba'a san me take fada ba.XS
SM
MD
LG