Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An dage Shari'ar tsohon shugaban Iraq sai Lahadi mai zuwa


A yau Talata an dage zaman sauraron shari’ar da ake wa tsohon shugaban kasar Iraq da mukarrabans su bakwai sai ranar Lahadi mai zuwa idan Allah ya kaimu. Wani mai Magana da yawun kotun Raid Judi ya fadawa manema labarai cewa kotun ta yanke shawarar dage ranar wannan shari’ar ne saboda wasu shedu da za su bayya a kotun basu je ba. Jiya Litinin ne kotun ta nada Raouf Rasheed Abdel Rahman wani ba kurde amatsayin alkalin wucin gadi da zai maye gurbin Alkalin da ke shari’a ada, wanda ya yi murabus a wannan wata bayan sukar da ya sha kan yadda yake tafiyar da shari’ar.

A bangaren tashe-tashen hankula da ake fama da su a kasar kuma, ‘yan bindiga sun kame wasu injiniyoyin kasar jamus 2 a wata matattar mai a garin Baiji dake arewacin birnin Bagadaza. A wani gefen kuma rundunar sojn Amirka tace an kashe sojojin Amirka biyu jiya Litinin lokacin da motar da suke cikinta ta taka wani bam da aka binne a gefen hanya. Sannan kuma wasu sojojin kundun balan Amirka biyu sun muta a wani hadarin Mota a yammacin kasar Iraq din.

XS
SM
MD
LG