Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta-Kifen Yankin Niger Delta Sun Kai Hari Kan Ofishin Wani Kamfanin Mai Suka Kashe Mutane Tara


Wasu ’yan bindiga sun kai hari a kan ofisoshin wani kamfanin mai na kasar Italiya a yankin Niger Delta, suka kashe mutane 9 suka sace wasu jakunkuna na kudi.

Kamfanin man mai suna ENI ya ce ya kwashe dukkan ma’aikatansa na wani dan lokaci daga ofisoshinsa dake birnin Fatakwal.

Kamfanin ya ce mutane da dama sun ji rauni a harin na ranar talata, amma ba a san adadinsu ba. Shaidu sun ce mutane 8 daga cikin 9 da suka mutu ’yan sanda ne.

Ba a san ko ’yan bindigar suna da alaka da ’yan dabar da suka kai hare-hare kwanakin baya a kan cibiyoyin mai har suka sace ’yan kasashen waje 4 suna yin garkuwa da su ba.

Wadancan 'yan dabar sun yi barazanar kai karin hare-hare a kan cibiyoyin mai har sai an sako wani shugabansu.

A halin da ake ciki, kungiyar agaji ta Red Cross ta kara matsa hannu a kokarin da take yi na ganin an kyale ta. domin ta gana da ’yan kasashen waje hudu ma’aikatan mai da ake yin garkuwa da su.

XS
SM
MD
LG