Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Rude Lokacin Da Aka Koma Shari'ar Saddam Hussein


Ba tare da wani bata lokaci ba shari'ar Saddam Hussein ta rikide ta koma cacar-baki a yayin da sabon alkalin dake jagorancin wannan shari'ar yayi kokarin yin tarnakin irin kalamun tsohon shugaban na Iraqi. Wakilin Muryar Amurka Ben Gilbert ya ce wannan shi ne zaman farko da kotun ta yi cikin wata guda.

A lokacin da aka fara zaman shari’ar ta lahadi, sabon alkalin kotun ya ce sam ba zai yarda da irin jawabai da take-taken da suka gudana a can baya ba. Nan da nan sai daya daga cikin wadanda ake tuhuma a shari’ar, Barzan al Tikriti, dan’uwan Saddam kuma tsohon darektan hukumar leken asirin kasar, ya kalubalanci alkali Raouf Abdul-Rahman.

Daga nan ne sai alkali Abdul-Rahman ya umurci al-Tikriti da ya fita daga cikin kotun. Da ya ki fita sai dogarawan kotu suka yi waje da shi. Lauyoyin dake kare wadanda ake tuhuma sun bayyana rashin yarda da wannan matakin, kuma domin nuna rashin jin dadinsu, sai suka tattara takardunsu suka fita daga cikin kotun.

A lokacin da aka kawo wasu lauyoyin dabam wadanda kotu ta nada da kanta domin su kare wadanda ake tuhuma, sai Saddam ya mike ya ce bai yarda ba, aka fara musanyar kalmomi masu zafi a tsakanin alkalin da tsohon shugaban.

Saddam dai ya fadawa alkalin cewar shekaru 23 yayi yana mulkin Iraqi, kuma shi alkalin talakansa ne. "Amma a yanzu kana son ka mayar da ni tamkar mai laifin dake kare kansa..." in ji Saddam.

Daga nan ne sai shi kuma alkalin ya ce, "nine alkali a wannan kotu, kuma kai ne ake tuhuma da laifi." A yayin da maganganu suka yi zafi, Saddam yayi ta buga kan tebur da hannunsa, yana neman da shi ma a kyale shi ya bar kotun. A fusace, Saddam ya ce, "ni fa na gaji da wannan kotun. Ina son a fitar da ni daga cikin wannan kotu yanzu yanzun nan."

Dogarawa sun raka Saddam da wani mutumin guda da ake tuhuma daga zauren kotun, aka ci gaba da zaman shari’ar. Daga cikin mutane 7 da ake tuhuma, 4 ne kawai suke kotu a lokacin.

Kafin a dage ci gaba da shari’a zuwa ranar laraba, kotun ta saurari wata mace wadda ta bayyana yadda a cewarta gwamnatin Saddam ta kashe mijinta da mahaifinta a 1982, a bayan da aka yi yunkurin kashe tsohon shugaban a garin Dujail.

Alkalin da ya jagoranci zaman kotun a ranar lahadi ya maye gurbin alkalin kotun na asali, Rizkar Mohammed Amin. Alkali Amin yayi murabus a watan nan a bayan da wasu jami’an gwamnati suka soki dari-darin da yake nunawa wajen rufe bakin wadanda ake tuhuma a kotun.

XS
SM
MD
LG