Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Olusegun Obasanjo Na Nijeriya Ya Lashi Takobin Murkushe Tashin Hankali A Yankin Niger-Delta


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya lashi takobin murkushe tashe-tashen hankula a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur, a bayan ganawar da yayi da wasu ma'aikatan mai su hudu wadanda aka shafe kwanaki 19 ana yin garkuwa da su.

Shugaba Obasanjo ya ce ba zai taba mika wuya ga hare-haren da ake kaiwa a kan kamfanonin mai ba.

Shugaban na Nijeriya yana bayyana wannan ne a ranar litinin lokacin da yake ganawa da ma'aikatan mai 'yan kasashen waje su hudu wadanda 'yan ta-kife suka sako su 'yan sa'o'i kadan kafin ganawar.

An bayar da rahoton cewa mutanen hudu (Ba Amurke, da dan Britaniya, da dan Honduras da mutumin Bulgariya) su na da alamun lafiya, amma kuma duk da haka likitoci za su duba su kafin su koma gida ga iyalansu.

Kungiyar daba yankin Niger-Delta mai suna "Movement for the Emancipation of the Niger Delta" (watau Kungiyar ceto yankin Niger-Delta a Hausance) ta ce ta sako mutanen da ta sacen ne a bisa "dalilai na jinkai."

Haka kuma, kungiyar ta yi barazanar ci gaba da kai hare-hare a kan cibiyoyin mai na Nijeriya. Ta ce tana gwagwarmaya ne domin maido da arzikin mai na yankin karkashin ikon mutanen yankin.

XS
SM
MD
LG