Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ethopia ta zargi Eritiriya da laifin kokarin tada fitina


Firayiministan kasar Ethopia, ya soki kasar Eritrea da laifin nuna jahilci da kuma yada jita-jitar barkewar yaki tsakaninsu, adaidai lokacin da rikicin kan iyaka tsakanin kasashen biyu take ci gaba da tsamari. A wani jawabi da yayi a Yau Alhamis a majalisar dokokin kasarsa, Firayiminista Melez Zenawi yace halin da kasar Eritrea take nunawa abu ne da zai iya janyo rikici tsakaninsu, sannan ya soki gwamnatin kasar Eritrea da kokarin cimma burinta ta hanyar aiki da karfin soja.

A ‘yan kwanakin nan cece-kuce tsakanin gwamnatocin kasashen biyu suna janyo fargabar barkewar wani sabon yaki tsakanin su. Su dai wadannan kasashe biyu sun fafata yaki na tsawon shekaru 2, a shekara ta dubu 2 ne suka daina yakin da ya ci rayukan mutane wajen dubu 70. Kasar Ethopia tace ta amince da shatin kan iyaka da wani kwamiti mai zaman kansa ya sharta musu bayan da suka kare yakin, to amma kasar tana son ayi wasu ‘yan gyare-gyare a tsarin da aka gabatar mata. Ita kuma kasar Eritrrea taki amincewa da duk wani mataki na diplomasiyya da za’a dauka domin warware wannan rikici nasu wanda ba zai sa kasar Ethopia ta fito fili ta nuna kan iyakar tsakaninsu domin a guji rikici nan gaba ba. Yau Alhamis, sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD, dake sa ido a bakin iyakar sunce akwai tankiya sosai tsakaninsu a bakin iyakar.

XS
SM
MD
LG