Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Ceto Su Na Ci Gaba Da Ayyukan Nemo Mutanen Da Suka Kubuta Da Rayukansu A Bahar Maliya


Kungiyoyin ceto su na ci gaba da binciken tekun Bahar Maliya, a bayan da wani jirgin ruwa na Misra ya nutse dauke da fasinjoji akalla dubu daya da dari uku da ma'aikata dari daya a dab da gabar kasar ta Misra. Hukumomi sun ce mutane akalla dubu daya sun mutu ko sun bace ya zuwa faduwar rana jiya jumma'a.

Ma'aikatar sufuri ta Misra ta ce an ceto mutane akalla dari uku, aka kuma tsinci gawarwakin mutane dari da tamanin da biyar ya zuwa faduwar ranar.

Gidajen telebijin sun nuna hotuna na ban mamaki inda jiragen saman helkwafta suke zakulo mutanen da suka kubuta da rayukansu daga cikin ruwan tekun bahar Maliya, wasu kuma a jikin kwale-kwalen roba.

Wasu jiragen ruwan ceto an Misra guda hudu sun isa wurin da aka yi wannan hatsari sa'o'i goma a bayan da wannan jirgin ruwan fito na fasinja mai nauyin ton dubu 12 ya bace daga na'urorin hango jirage alhamis da maraice.

Gwamnan lardin Bahar Maliya, Abubakar el-Rashidi, ya shaidawa Muryar Amurka cewar dare ba zai sa a katse aikin ceton da ake gudanarwa ba. "Har yanzu ana ci gaba da ayyukan ceto, kuma in sha Allahu za a ci gaba da ayyukan babu tsattsayawa" in ji shi.

Hukumomi sun ce wannan jirgin ruwa dake dauke da ma'aikata dake komowa daga Sa'udiyya, yana dauke da motoci fiye da dari biyu a lokacin da ya bar tashar jiragen ruwan Dubah na Sa'udiyya ranar alhamis da maraice a kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwan Safiaga a Misra.

Har yanzu ba a san abinda ya haddasa wannan mummunan hatsari ba. Amma kuma iska tana kadawa da karfi, igiyoyin ruwa su na motsawa da karfi yayin da aka ce akwai guguwa irinta rairayin hamada a gabar Sa'udiyya ranar alhamis da maraice.

Gwamnan lardin na Bahar Maliya, el-Rashidi, ya ce an kaddamar da aikin ceto tun safiyar jumma'a a bayan da hukumomi suka fahimci cewar jirgin bai iso a kan lokacin da ya kamata ya isa ba. Rahotanni daga yankin na Bahar Maliya ya ce iska mai kadawa da karfi da kuma munanan igiyoyin ruwa sun kawo cikas ga yunkurin farko da aka yi na aikin ceto.

Andrea Odone jami'i ne na kamfanin safarar jiragen ruwa mai suna "El-Salam Maritime Transport" wanda ya mallaki wannan jirgin ruwa da ya nutse. Ya ce da alamun jirgin ya nutse haka kwatsam ba tare da gargadi ba. "Ba a samu sakon neman agajin gaggawa daga jirgin ba. Taurarin dan Adama ma ba su ga wani sakon neman agaji daga jirgin ba" in ji shi.

Kamfanonin yada labarai sun ce da gaske ne ba a samu wani sakon neman agaji a dukkan gabobi guda biyu na tekun Bahar Maliya ba. Amma kuma kamfanin dillancin labaran gabas ta tsakiya, MENA, ya ce wani jirgin ruwan fito mai suna St. Catherine, ya samu sakon neman agajin gaggawa daga kyaftin an jirgin da ya nutse. Ba a san irin matakin da jirgin na St. catherine ya dauka daga nan ba.

Har ila yau, wani sansanin mayakan sama na Britaniya dake Scotland, ya ji sakon neman agajin gaggawa daga jirgin, ya kuma aike da wannan sako ga hukumomin misra ta hannun Faransa. Andrea Odone na kamfanin el-Salam ya ki bayyana hasashensa kan yadda hatsarin ya abku.

"Ba mu da wani bayani, haka kuma ba zamu iya tabbatar da ko kwale-kwalen roba na ceton rai guda nawa ne jirgin ya iya kaddamarwa kafin ya nutse ba,: in ji Mr. Odone. "Abinda zamu iya cewa shi ne jirgin yana dauke da kayan ceton rayukan fasinjoji fiye da dubu biyu. Amma a yanzu ba zamu iya cewa ga abinda ya faru ba."

Hukumomin Misra sun kaddamar da bincike dangane da wannan hatsari. Wani kakakin shugaba Hosni Mubarak ya ce da alamun akwai matsalar kula da lafiyar jama'a ganin yadda jirgin ruwan ya nutse cikin gaggawa haka.Ya kuma ce watakila dai babu wadatattun kwalekwalen roba a cikin jirgin ruwan.

Wani jirgin ruwan na kamfanin el-Salam ya nutse a cikin watan Oktoba a bayan da ya ci karo da wani jirgin ruwan 'yan kasuwa na kasar Cyprus. Mutane biyu suka mutu a wannan hatsarin.

XS
SM
MD
LG