Dukkan mutane ashirin dake cikin wani jirgin saman soja na kasar Sudan sun mutu a lokacin da jirgin yayi hatsari yayin da yake sauka ranar asabar a yankin kudancin Sudan.
Jami'an rundunar sojojin Sudan sun ce tayar gaba ta jirgin ta fashe a lokacin da ya zo sauka, abinda ya sa jirgin ya kauce daga kan hanyar saukarsa ya kuma yi bindiga.
Wannan hatsari ya faru jiya asabar da safe a garin Aweil, kilomita dari takwas a kudu maso yamma da Khartoum, babban birnin kasar.
Akwai ma'aikata bakwai da kuma fasinjoji goma sha uku a cikin jirgin.