Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Zata Hana Sabuwar Gwamnatin Falasdinawa Da Hamas Ke Jagoranci Miliyoyin Daloli


Isra'ila ta kafa takunkumin tattalin arziki a kan sabuwar gwamnatin Falasdinawa, kwana guda a bayan da 'yan kungiyar Hamas suka karbi ragamar jagorancin gwamnatin. Majalisar ministocin Isra’ila ta yanke shawarar dakatar da mayarwa da majalisar mulkin kan Falasdinawa dala miliyan 50 na harajin da Falasdinawa ke biya kowane wata.

Mai rikon mukamin firayim ministan bani Isra’ila, Ehud Olmert, ya ce Isra’ila ba zata yi hulda da kungiyar dake neman shafe kasar ta yahudawa daga bangon duniya ba. Ya ce, "Majalisar mulkin kan Falasdinawa ta zamo gwamnatin ta’addanci da yake yanzu Hamas ce ke jagorancinta. Isra’ila ba zata amince da haka ba."

Majalisar ministocin ta bani Isra’ila ta yi kira ga Amurka da Turai da su bi sahunta wajen tsinke agajin kusan dala miliyan dubu daya da suke bai wa majalisar mulkin ta Falasdinawa a kowace shekara. A daidai wannan lokacin kuma, Isra’ila ta yi na’am da rokon da Amurka ta yi mata na kada ta dauki tsauraran matakai, kamar killace zirin Gaza da nufin nakkasa dukkan harkokin tattalin arziki.

Sai dai kuma, majalisar ministocin ta ki amincewa da shawarar da ma’aikatar tsaro ta bayar ta hana dubban Falasdinawa ma’aikata shiga Isra’ila tare da hana kayayyaki shiga cikin Isra’ila daga Gaza.

Mark Regev shi ne kakakin Isra’ila. Ya ce, "Isra’ila ba zata yi wani abinda zai gurgunta agajin jinkai ga al’ummar Falasdinawa ba."

Kungiyar Hamas ta bayyana takunkumin kudin da Isra’ila ta yi mata a zaman matakin kusa, ta kuma yi watsi da kiraye kirayen da kasashen duniya suka yi mata na cewar ta yi tur da tashin hankali ta amince da Isra’ila a zaman kasa.

Abdel Aziz Duweik na kungiyar Hamas shine sabon kakakin majalisar dokokin Falasdinawa. Ya ce, "zamu ci gaba da yin gwagwarmaya da mamaye yankunanmu da bani Isra’ila ta yi, kuma a wasu lokutan tilas ne mu yi ko oho da abinda duniya zata ce."

Hamas ta zabi Isma’il Haniyeh mai shekaru 43 da haihuwa ya zamo sabon firayim ministan Falasdinawa. Ana daukarsa a zaman shugaban bangaren kungiyar wadda ta fi sanin ya kamata, kuma yana da dangantaka mai kyau da jam’iyyar Fatah mai sassaucin ra’ayi, wadda aka kayar a zabe. Malam Haniyeh ya ce a yau litinin Hamas zata fara tattauna kafa sabuwar gwamnati.

XS
SM
MD
LG