Yawan mutanen da aka kashe a rikicin addinin da aka shafe kwanaki biyar ana yi a tsakanin Musulmi da Kirista a Nijeriya ya tashi zuwa akalla sittin da hudu, a bayan kashe-kashe na baya-bayan nan a kudancin kasar.
Larabar nan, gungu-gungun Kiristoci a Anaca, sun kashe mutane goma sha tara, akasarinsu Musulmi. Shaidu na gani da idanu sun bayyana yadda jini yayi ta malala, inda Kiristoci masu zanga-zanga suka yi amfani da adduna wajen datsewa tare da sassare mutane. A wani lokacin ma sai da sojoji suka yi amfani da karfi kan 'yan zanga-zangar domin hana su kai karin hare-hare.
Tashin hankali na garin Anaca ya faro ranar talata a lokacin da aka kashe mutane akalla goma sha biyu a hare-haren da Kiristoci suka kai kan Musulmi.
Wannan tashin hankalin na Anaca, daukar fansa ce ta hare-haren da aka kai kan Kiristoci a yankin arewacin kasar inda Musulmi suka fi yawa. An kashe mutane akalla talatin da uku, akasarinsu Kiristoci, a lokacin da Musulmi suka tayar da fitina a biranen Bauchi da Maiduguri na arewacin kasar a farkon mako.
Fitina bta samo asali daga Maiduguri a lokacin wata zanga-zangar da Musulmi suka shirya ta nuna kyamar zane-zanen batunci na Annabi Muhammad (saw).
Tashin hankalin addini dai ba sabon abu ba ne a Nijeriya a tsakanin Musulmi dake da rinjaye a arewa da Kiristoci wadanda suka fi yawa a kudancin kasar.