Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madagascar Ta Tabbatar Da Bullar Wata Cutar Da Sauro Ke Yadawa


Madagascar ta tabbatar da bullar wata cutar da sauro ke yadawa, wadda ta kama mutane fiye da dubu dari da tamanin a fadin yankin tekun Indiya.

Jami'an kiwon lafiya a Madagascar sun ce sun ga mutane jefi-jefi da suka kamu da wannan sabuwar cuta da ake kira "CHIKUNGUNYA" amma kuma ba su bayar da takamammen adadin mutanen da suka kamu ba.

Kwararru sun ce wannan cuta tana janyo zazzabi mai zafi da kuma zogi mai tsanani, sannan har yanzu ba a san maganinta ba.

Jami'ai sun ce mutane casa'in da uku sun mutu daga wannan cuta a tsibirin Reunion na Faransa, mai tazarar kilomita dari takwas a gabas da Madagascar. An ce a cikin shekara gudan da ta shige, cutar ta kama kimanin kashi 20 cikin 100 na mutanen tsibirin Reunion.

Har ila yau an bayar da rahoton bullar cutar a sauran tsibiran dake tekun Indiya, ciki har da Mayotte da Seychelles.

XS
SM
MD
LG