Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar white House ta yi kira akan a sake zabe a Belarus


Fadar White House ta shugaban Amirka tayi watsi da nasarar da shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya sake samu a zabenda akayi a kasar, sannan tayi kira akan asake zaben. Kakakin fadar White House Scott McClellan ya dai cewa zaben da akayi a ranar Lahadi anyi murdiya sosai a lokacinsa saboda abinda ya kira yayanin razanarwa da akayi zaben a ciki. Jami'an tarayyar Turai da suka kalli yadda aka gudanar da zaben sunyi tir da shi. sunce matakan razana jama'a da kuma yadda akayi ta bi ana kama magoya bayan 'yan adawa ana tsaresu, sun taru sun lalata zabe. Kwamishina mai lura da al'amurran cikin gidan tarayyar Turai Benita Ferrero-Weldner ta fada cewa ga dukkan alamu, za'a dauki matakan ladabtar da manyan jami'an gwamnatin Belarus a haramta musu biza da sauransu.

XS
SM
MD
LG