Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'yan Shi'a aIraq sunyi aduo'i don Tunawa da....


'Yan shi'a a Iraq masu ibada sun yi dafifi a wajen adduo'i domin tunawa da Imam Husain a birnin karbala duk da tsauraran matakan tsaro da aka dauka. Hukumomin Iraq sun tura karin jami'an tsaro a cikin da zagayen birnin Barkaba domin kokarin hana sake barkewar hargitsi irin wanda ya afku a shekata ta 2004 da 'yan ta'adda suka yi amfani da lokacin wajen kai hari. Mutane sama da 170 suka halaka a wancan bikin. 'Yan Shi'a masu ibada sunyi ta gilmawa ayari ayari suna shiga birnin Karbala tun tsakiyar makon jiya don haka yanzu birnin ya cika makil. Daga cikin ayyukan ibadar 'yan shi'ar a karbala harda daure kansu da sarka domin tunawa da yadda Iman Hussain ya yi gwagwarmaya da hakan nuna cewar an kawo karshen zaman makokin kwanaki 40.

XS
SM
MD
LG