Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Tana Kidaya Jama'arta


A yayin da Nijeriya ta kaddamar da aikin kidaya jama'arta na farko cikin shekaru 15 daga yau talata, hukumomi su na fatar tantance gaskiyar yawan jama'ar kasar. Sai dai kuma, wakilin Muryar Amurka Gilbert Da Costa, ya ce akwai matsaloli da yawa da zasu iya gurgunta aikin kidayar.

A can baya, an zargi gwamnatoci da laifin tabka magudi wajen bayyana adadin yawan jama'a domin cim ma wasu gurori na siyasa. Gwamnatin tarayya a Nijeriya tana rarrabawa jihohi kudi ne ta yin la'akari da yawan jama'arsu.

A wani yunkurin kawar da hauragiyar kabilanci ko ta adini daga cikin wannan aiki, gwmnatin Nijeriya a wannan karon ta cire duk wata tambayar da ta shafi addini ko kabilar mutum.

Har ila yau, an tura jami'an kidaya nesa da jihohinsu domin gudanar da wannan aiki. Shugabannin al'ummar Kiristoci musamman sun nuna rashin jin dadi da cire tambaya kan addini a lokacin kidayar.

Sai dai kuma karuwar tankiyar siyasa yayin da aka doshi babban zabe a cikin shekara mai zuwa, tana yin barazana ga sahihancin wannan kidaya.

Nijeriya tana da kabilu kimanin dari biyu da hamsin, kowaccensu tana neman a ba ta damar taka rawa a harkokin siyasar kasar. Wasu al'ummomin sun ki amincewa da jami'an kidaya da aka tura yankunansu, su na masu bukatar da a nada mutanen yankinsu kawai.

Amma duk da irin wannan kalubale wajen gudanar da kidaya amintacciya a Nijeriya, shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa, Sama'ila Makama, ya fadawa Muryar Amurka cewa a shirye hukumarsa btake domin gudanar da wannan aiki na tsawon kwanaki biyar da aka fara yau talata.

Shugaban hukumar ya ce har ya zuwa lokacin da yake magana, babu wani rahoton da aka samu na matsala ko barazanar kauracewa aikin. A maimakon haka ma, in ji shi, shugabannin al'umma su na ci gaba da yin kira ga jama'arsu da su tabbatar an kidaya su.

An dauki ma'aikatan kidaya kimanin dubu dari takwas da ashirin domin wannan aikin. An kiyasta cewa Nijeriya zata kashe kudi kimanin dalar Amurka miliyan dari biyu da sittin. Tarayyar Turai, wadda ta aike da 'yan kallo casa'in, ta bayar da gudumawar dala miliyan dari da hamsin.

Kidaya ta baya da aka gudanar cikin shekarar 1991, ta ce Nijeriya tana da mutane miliyan tamanin da takwas da rabi. A bisa kiyasin cewa ana samun karuwar kashi uku daga cikin dari na jama'a a Nijeriya kowace shekara, ana kyautata zaton yawan 'yan Nijeriya zai kai miliyan dari da ashirin zuwa miliyan dari da hamsin a yanzu.

XS
SM
MD
LG