Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

shugaba Musharraf ya kori bakin 'yan gwagwarmaya a kasarsa


Shugaban kasar Pakistan Pavel Musharraf ya umurci ‘yan gwagwarmaya na kungiyar alka’ida baki, da su fice masa daga cikin kasa imba haka ba kuma sojojinsa za su kasha su. Ya fadawa wani taro a tsakiyar birnin Lahore ran Alhamsi cewa mayakan sa- kai baki suna aikata ta’addanci ba’a cikin kasarsa kadai ba harma da sauran kasashen duniya.

Janar Musharraf yace ba zai kyale baki ‘yan ta’adda da masu tsananin ra’ayi su rika buya cikin kabilun kasarsa dake tsakanin tsaunuka ba. Ana jin akwai dururuwan mayakan Taleban da Alqa’ida sun sulale sun shiga tsakanin kabilun kasar dake zaune a tsaunuka a bakin iyakokin kudu da arewacin kasar.

Kasar Pakistan tace ta tura sojojinta wajen dubu 80 zuwa kan iyakar kasar a ‘yan watannin nan kuma sun kai sumame a mafakar mayakan sa kan inda suka kashe daruruwansu.

XS
SM
MD
LG