Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sako  Jill Carroll da akayi garkuwa da ita a Iraq


A kasar Iraq, ‘yan bindigan nan da suka kama wata ‘yar jaridar kamfanin jaridar Christians Science Monitor, Jill Caroll, sun sako ta jiya Alhamis bayan kusan watanni uku da sace ta. Jiya Alhamis Jill Carroll ta fadawa wani gidan Talbijin na kasar Iraq cewa ba wanda ya taba lafiyarta, kuma ana bata abinci akai akai ana kuma barinta tayi duk abinda take bukata a inda aka tsareta. Jakadan Amirka a birnin Bagadaza Zalmay Kazilzad yace jami’an Amirka da na Iraq basu da hannu a sakin wannan budurwa. Ada dai wadanda suka saceta sun yi barazanar kashe idan ba'a saki duk matan Iraq da ake tsare dasu a gidajen kurkukun kasar Iraq ba.

XS
SM
MD
LG