Paparoma Benedict ya karamta magabacinshi paparoma John Paul II wanda ya rasu bara.
Paparoma Benedict ya yabi magabacinshi domin yayata akidar ƙauna da bege da ya yi dukan rayuwarshi a matsayin paparoma ya kuma bayyana irin rayuwa abin koyi da paparoma John Paul ya yi a kwanakinshi na ƙarshe a duniya.
Paparoma Benedict ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi daga tagar fadar Vertican ga dubban mahajjata da suka taru a filin St Peters Square. Inda aka yi addu’oi na musamman domin tunawa da marigayin.
Paparoma John Paul ya rasu ne ranar 2 ga watan Aprilu bata yana da shekaru 84 a duniya ya kuma shafe shekaru 26 a matsayin paparoma. Yana ɗaya daga cikin shugabannin da mabiya ɗarikar katolika suka fi kauna.