Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Mataimakin Shugaban Afirka Ta Kudu Ya Fara Bayar Da Shaida A Shari'ar Fyade Da Ake Yi Masa


Tsohon mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya fara bayar da shaida a shari'ar da ake yi masa ta fyade ma wata mai abota da iyalansa.

A lokacin da yake bayar da shaidar yau litinin a wata kotun birnin Johannesburg, Zuma ya musanta zargin da wannan mace mai shekaru 31 da haihuwa ta yi, yana mai fadin cewa lallai yayi jima'i da ita a bara amma da yardarta.

Ya kara da cewa mahaifin matar dake zarginsa babban abokinsa ne, ya kuma ce su biyun manyan 'ya'yan jam'iyyar ANC ne.

Amma kuma Zuma ya musanta cewar dangantakar dake tsakaninsa da wannan mace tamkar ta 'ya da uba ne.

Har ila yau Mr. Zuma, mai shekaru 63 da haihuwa ya ce yayi imani wannan tuhuma ta fyade da ake yi masa wata makarkashiya ce ta gurgunta fatarsa ta yin takarar kujerar shugaban kasa.

A da ana daukar Mr. Zuma a zaman jagora cikin mutanen da zasu gaji shugaba Thabo Mbeki, kafin a kore shi daga kan mukamin mataimakin shugaban kasa a bara bisa zargin zarmiya da cin hanci.

XS
SM
MD
LG