Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun dake shari‘ar tsohon shugaba Saddam Hussain ta kammala zaman yau kuma kotun ta kori lauyan Saddam Hussain daga harabar kotun saboda rashin da’a.


Kotun dake shari‘ar tsohon shugaba Saddam Hussain ta kammala zaman yau talata, amma kafin ta fara sauraren shari‘ar a yau saida kotun ta kori lauyan Saddam Hussain daga harabar kotun saboda rashin da’a. Alkalin kotun ya kori Lauya Bushra Khalil a zaman kotun na yau laraba bayan da ta riƙa ihu tana daga murya tare da nuna wasu hotunan fursunonin da ake tsare dasu a Kurkukun Iraqi tana zargin cewa sojin Amurka ne ke wulakanta fursunonin Iraqi.

A zaman kotun na yau laraba, Saddam Hussain ne kadai aka yiwa tambayoyi game da rawar da ya taka a kisan gillar da ake zargin yasa an yiwa ’yan Shi’a sama da 140 a shekarar 1982. Amma da yake kare kansa a kotun, tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussain, ya la’anci Ma’aikatar gidan Iraqi da ’yan Shi’a ke gudanarwa, ya la’anci irin yadda jami‘an kurkukun Iraqi ke azabtar da ’yan Iraqi. Sannan yayi kira ga kasa da kasa da su taimaka su binciko ainihin sa hannun daake zargin nasa a kan daftarin dokar bada iznin a yiwa ’yan shi’a kisan gilla, domin yace tana yiwuwa masu gabatar da mai laifi gaban shari’a sun saci sa hannunsa ne domin gabatar da shaida.

Lauyoyin dake gabatar da mai laifi gaban shari’a sun tabbatar dacewa sa hannun Saddam Hussain ne a kan daftarin dokar bada iznin kisan gillar ’yan Shi’a a kauyen Dujail na kudancin Iraqi.

XS
SM
MD
LG