Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amirka ta roki 'yan kasar Iraq su yiwa Allah su kai zuciya nesa..


Amirka tayi kira ga ‘yan kasar Iraq akan su yiwa Allah da Annabi su kai zuciya nesa sabili da fashewar wani Bam da ya kashe mutane 10 a kusa da wani masallacin‘yan Shi’a a kudacin birnin Najaf. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amirka Sean McCormick yace wadanda suke kai hari a wuraren ibada, masu gaba ne da addini da kuma rayuwar bani adama.

Jiya Alhamis ne Bam din ya fashe a kusa da Hubbaren Imam Ali, daya daga cikin muhimmanci wurare masu tsarki inda ‘yan shi’a suke zuwa ibada. Haka kuma a jiyan firayi-ministan Iraqi Ibrahim Aljafari, wanda ruwan rikici ya ke neman lashewa ya sake nanata anniyarsa ta kin sauka daga karagar mulkin kasar a don ya tsaya takaran wannan mukami a karo na biyu. Yace ba zai sauka ba sai in majalisar dokokin kasar ta bukaci yayi hakan.

Matsayinsa na dan takaran wannan mukami a karo na biyu shine ginshikin rikicin da ya hana kafa gwamnatin hada kan al’umar kasar yau wajen watanni hudu kenan bayan zaben kasar. Shugabannin kurdawan da larabawan 'yan Sunni sunce Ibrahim Aljafari bai taka wata rawar gani ba wajen kawo karshen tashe tashen hankulan kasar.

XS
SM
MD
LG