'Yan siyasar Sunni da na Kurdawan kasar Iraqi sun sake bayyana rashin yardarsu da nada firayim minista Ibrahim al-Jaafari domin ya ci gaba da rike wannan kujera a sabuwar gwamnatin da ake shirin kafawa.
Wannan shawara ta su, ta zo a bayan da babbar gamayyar 'yan mazhabin Shi'a ta Iraqi ta kafa wani kwamitin da zai yi kokarin lallashin sauran jam'iyyu su goyi bayan al-Jaafari. Gamayyar ta 'yan Shi'a ita ce mafi girma a majalisar dokoki, amma kuma tana bukatar kuri'un 'yan Sunni da na Kurdawa domin cimma rinjayen da zai sa ta iya kafa gwamnati.
Shugabannin Shi'a su na sake ganawa a yau domin yanke shawarar irin matakan da zasu dauka a gaba. Yau watanni hudu ke nan su na kokarin kafa gwamnati. Amma kuma sabanin ra'ayi a kan Ibrahim al-Jaafari yana kawo musu cikas.
Shugabannin Kurdawa da na 'yan mazhabin Sunni sun ce firayim ministan bai dauki matakai masu nagarta na kawo karshen tashin hankali ba.