Sojojin gwamnati sun kara daukar matakan tsaro a N’Djamena, babban birnin Chadi, a yayin da majiyoyin tsaro suka ce ’yan tawaye sun doshi birnin.
An tsinke layukan wayoyin tarho na hannu, mobayil ko salula, yayin da wani wakilin Muryar Amurka a babban birnin ya ce ofisoshin jakadancin kasashen waje sun shawarci ’yan kasashensu da su guji fita daga cikin gidajensu.
Ma’aikatar tsaro ta Faransa ta ce zata tura karin sojoji dari da hamsin domin tallafawa sojojinta su dubu daya da dari biyu dake Chadin tuni. Gidan rediyon Faransa ya fada a yau laraba cewa sojojin zasu zauna cikin shirin kwashe ’yan kasashen waje idan bukatar hakan ta taso.
Wannan farmaki na kungiyar ’yan tawayen Hadaddiyar Kungiyar Kawo Sauyi ya zo kasa da wata guda kafin a gudanar da zaben shugaban kasa. ’Yan tawayen su na kokarin hambarar da shugaba Idris Deby.
Ba a san yawan ’yan tawayen da suka doshi birnin N’Djamena ba, ko kuma tazarar dake tsakaninsu da birnin.