Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamun Hakar Firayim Minista Silvio Berlusconi Na Italiya Ba Za Ta Cimma Ruwa Ba


Da alamun kalubalantar sakamakon zaben 'yan majalisar dokoki na wannan mako da firayim minista Silvio Berlusconi na Italiya yake yi, ba zata je ko ina ba, a yayin da alkalai suke ci gaba da sake kidaya dubban kuri'un da ake gardama a kansu.

Kafofin labarai na Italiya sun bayar da labarin cewa sake kidaya kuri'un da alamun ba zai sauya sakamakon zaben da aka bayar ba. gamayyar jam'iyyun gurguzu masu ra'ayin sassauci ta shugaban adawa Romano Prodi, ta samu rinjaye a dukkan majalisu biyu na dokokin tarayya, amma kuma rinjayen kuri'un nata bai taka kara ya karya ba a karamar majalisar dokokin.

Har ila yau, jaridu sun ce yawan kuri'un da ake gardama a kansu ba su kai dubu arba'in da uku kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta fada tun fari ba.

Wasu magoya bayan Mr. Berlusconi sun yi ikirarin cewa akwai wasu kuri'u dubu hudu da ya kamata a ce na firayim ministan ne. Amma sauran kawayen firayim ministan sun fara bayyana tababar cewa sake kidayar da ake yi zai iya ba shi nasara a zaben.

XS
SM
MD
LG