Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Jinkirta Zaman Majalisar Dokokin Iraqi da Aka shirya Gudanarwa Litinin


Shugabannin Iraqi sun jinkirta wani zaman majalisar dokokin da aka shirya gudanarwa yau litinin, a saboda gardamar da ake ci gaba da yi a kan ko wanene zai jagoranci sabuwar gwamnati.

Manyan jam’iyyun kasar su na fuskantar cikas kan wannan batu tun cikin watan Disamba.

’Yan Shi’a, wadanda ke da rinjaye a majalisar dokoki, sun ki yarda da bukatun Larabawa ’yan Sunni da na Kurdawa a kan su zabi wani mutum dabam ya haye kan kujerar firayim minista, ba mai ci yanzu ba, watau Ibrahim al-Jaafari.

Jakadan Iraqi a Amurka, Samir Sumaidaie, ya ce an fara ganin alamun sasantawa. Wasu jami’ai sun ce watakila ’yan Shi’a zasu gabatar da sunan Ali al-Adib daga jam’iyyar malam Jaafari.

A ci gaba da tashin hankali kuma, sojojin Iraqi da ’yan tawaye sun gwabza yau litinin da sanyin safiya a wata gunduma ta ’yan Sunni dake arewacin Bagadaza. Haka kuma, ’yan sandan Iraqi sun gano gawar dan’uwan wani babban dan siyasa dan Sunni, makonni uku a bayan bacewarsa. ’Yan sanda suka ce an harbi Taha al-Mutlaq a kai da bindiga.

XS
SM
MD
LG