Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Jam'iyyar Hamayya Ta Kasar Liberiya Ta Ce Zata Kai Karar Gwamnati


Babbar jam'iyyar hamayya ta kasar Liberiya ta ce zata kai karar gwamnati a saboda abinda ta kira, kamawa da kuma tsare shugabanta, George Weah, da aka yi na wani dan lokaci.

Jam'iyyar "Congress for Democratic Change" ta ce an fito daga George Weah da wasu jami'ansa su hudu daga cikin wani jirgin sama a ranar lahadi, aka tsare su na wani dan lokaci a saboda su na rike da takardun fasfo na jami'an diflomasiyya.

Weah ya sha kaye a hannun Ellen Johnson-Sirleaf, a zaben shugaban kasar da aka yi cikin shekarar da ta shige a Liberiya.

Jam'iyyarsa ta CDC ta ce jami'an da suka kama shi su na da alaka da shugaba Sirleaf, kuma gwamnatin tana kokarin kunyata Mr. Weah ne.

Amma kuma ministan yada labarai na gwamnati, Johnny McCain, ya ce ba a kama Mr. weah ko mukarrabansa a lokaxcin ba.

Ya ce biyu daga cikin mukarraban Mr. Weah su na rike da takardun fasfo na jami'an diflomasiyya, abinda bai kamata ba tun da basu da wannan matsayi. ya ce a lokacin da jami'an tsaro suka bukaci wadannan mutane biyu su fice daga cikin jirgin, sai shi ma Mr. Weah ya fice domin radin kansa.

XS
SM
MD
LG