Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Motar Tsohon Shugaban Tanzaniya Ta Kara Da Ta Jerry Rawlings A Afirka Ta Kudu


An bayar da rahoton cewa tsohon shugaban kasar Tanzaniya yana murmurewa a bayan da ya kubuta daga wani mummunan hatsarin mota a birnin Johannesburg a Afirka ta Kudu.

Tsohon shugaba Ali Hassan Mwinyi yana cikin wata kwambar motocin tsoffin shugabannin Afirka su 10 ne a lokacin da motarsa ta kara da motar dake dauke da tsohon shugaban kasar Ghana, Jerry Rawlings da mai dakinsa, Nana.

An dauki Mr. Mwinyi da Madam Nana zuwa wani asibitin birnin. An duba Mr. mwinyi aka sallame shi, yayin da aka yi wa Mrs. Rawlings aikin kananan raunukan da ta samu.

Kafofin labarai na Afirka sun ce hatsarin ya abku ne a lokacin da motocin dake cikin wannan kwamba suke kokarin kaucewa wani hatsarin dabam da ya faru a kan hanyarsu.

Tsoffin shugabannin su na kan hanyarsu ta zuwa wurin wani taro ne da aka kira da nufin tattauna hanyoyin karfafa zuba jari a kasashen Afirka da kuma martabar Afirka a kafofin labarai na Amurka.

XS
SM
MD
LG