Jami’an ayyukan ceto a Misra sun ce mutane akalla 22 sun hallaka a wasu fashe-fashe guda uku a birnin yawon shakatawa na Dahab a kasar. Wasu rahotannin sun ce yawan wadanda suka mutu ya zarce hakan.
Jami’ai suka ce wasu mutanen su akalla 150 sun ji rauni a fashe-fashen na maraicen yau litinin. Babu wani bayani gamsasshe kan kasashen mutanen da suka mutu a wannan lamarin.
Kafofin labarai sun ce fashewa guda ta abku a wani hotel, wata kuma a cikin kasuwa a wannan birni mai farin jini dake cike makil da ’yan yawon shakatawa da bude idanu. Shaidu sun ce motocin jigilar marasa lafiya da ’yan sanda su na kwarara cikin birnin a yanzu haka.
Babu wanda ya dauki alhakin kai hare-haren.
Birnin Dahab yana mashigin ruwan Aqaba, a bangaren gabashin zirin Sinai, ko Sinina. Wannan birni yana da farin jini ga baki ’yan kasashen waje, cikinsu har da ’yan Isra’ila. Jami’an Isra’ila sun ce ba su da wani labarin ko akwai wani dan kasarsu da ya ji rauni a lamarin. Isra’ila ta gabatar da tayin tura ma’aikatan gaggawa domin su taimaka wajen ayyukanceto.
A bara, hare-haren bam sun kashe mutane 60 a garin shakatawa na Sharm el-Sheikh dake bakin gabar bahar Maliya.