Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya ta amince zata sayarwa kasar Sin lasisin hakar Man Fetur hudu


Nigeria ta amince akan zata baiwa kasar Sin lasisi 4 na hakar mai a kasar yayinda ita kuma kasar China ta yi alkawari zata zuba jari na dala miliyon dubu 4 a fannin kayakin kyautata rayuwa a Nigeria. Jami’an Nigeria ne suka bada wannan sanarwa jiya Laraba adaidai lokacin da shugaban na Sin Hu Jintao ya fara ziyara aiki ta kwanaki biyu a kasar a wani bangare na ziyarar da zai kai kasashen Afrika.

A karkashin wannan yarjejeniya dai, Nigeria zata baiwa kafamin hakar mai na kasar China National Petroleum Corporation ‘yancin mallakar izinin hakar mai shi kadai a wurare hudu dake da albarkatun Man Fetur a lokacin da za ta yi gwanjon wuraren a watan Gobe.

Biyu daga cikin yankunan hakar Man suna yankin nan nai arzikin Man Fetur na Neja Delta. Sannan sauran wurare biyun kuma suna yankin nan na bakin tafkin Chadi wanda ba’a fara hakar Mai a kansaba. Makasudin wannan ziyara ta Shugaban na kasar China a Afrika shine ya samo mai da kuma kara bude hanyoyin ciniki da kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG