Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban  hukumar Nukiliyar kasar Iran ya gana da Mohammed Albaradei a Vienna


Babban Jami’in Nukiliyar kasar Iran ya gana a birnin Vienna tare da shugaban hukumar kula da makamashin Atomic ta kasa da kasa IAEA, ana saura ‘yan kwanaki kafin hukumar ta gabatar da rahoto akan shirye-shiryen nukiliyar Iran.

Jami’an Diplomasiyya a Viennan sun ce ba su yi tsammani an cimma wani matsayi na kirki a ganawa tsakanin jami’an biyu, Gholamreza Aghazadeh da Mohammed Elbaradei ranar Laraba ba.Yau jumma’a ce wannan hukuma ta Majalisar Dinkin Duniya zata gabatar da rahoto akan ko kasar Iran tana aiki da sharadin da kwamitin sulhu na Majalisar ya kafa mata akan ta dakatar da duk wani aiki na sarrafa makasahin karfen Uranium, ko kuma a’a. dan an sami Iran ta keta haddin wannan sharadi, kwamitin sulhun na iya saka mata takunkumin karya tattalin arziki.

Tun da fari a ranar Laraban, shugaban Addinin Iran Ayatolah Ali Khameni ya yi gargadin cewa za su yiwa kadarorin amirka aduk inda suke a duniya lahani idan Amirka ta kai hari akan kasar Iran. A wani mataki na maida martini kuma, ma’aikatar harkokin wajen Amirka ta shawarci kasar Iran akan ta ta yi amfani da diplomasiyya wajen warware wannan sarkakiyar, kuma ta yi gargadin cewa halin nuna tsageranci na iya harzuka kwamitin sulhu ya dauki matakin tattaunawa wajen neman hanyar da za’abi da kasar Iran.

XS
SM
MD
LG