Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce Rasha Da Sin Sun Tabbatar Masa Da Cewa Zasu Yi Adawa Da Duk Wani Yunkurin Kafawa Iran Takunkumi


Ministan harkokin wajen Iran ya ce kasashen Rasha da Sin sun tabbatar masa da cewa zasu yi adawa da duk wani shirin sanyawa Iran takunkumi a kan shirinta na nukiliya.

Manouchehr Mottaki ya fadawa wata jaridar kasar Iran mai suna "Kayhan" cewar jami'an diflomasiyya na kasashen biyu su na adawa da takunkumin tattalin arziki ko kuma daukar matakan soja a kan kasar Iran.

An buga wannan hira a yau talata, a daidai lokacin da jami'ai daga Rasha da Sin da sauran kasashe masu kujerun dindindin a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya tare da kasar Jamus suke ganawa a Paris a kan batun Iran.

Ana sa ran cewa Britaniya da Faransa za su gabatar da wani kuduri a gaban Kwamitin Sulhu nan gaba cikin wannan mako da nufin matsawa Iran lamba a kan ta daina gudanar da ayyukan nukiliya masu nauyi da take yi.

A wani labarin kuma, shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta kasar Iran, Gholam Reza Aghazadeh, ya ce kasarsa ta tace karfen Uranium wanda tsarkinsa ya kai kashi hudu da digo takwas a cikin dari. Ya ce Iran ba ta da wani shirin tace karfen Uranium wanda tsarkinsa zai wuce kashi biyar daga cikin dari. Ana bukatar a tace karfen Uranium wanda tsarkinsa ya kai kashi tamanin daga cikin dari kafin a iya kera bam na nukiliya da shi.

XS
SM
MD
LG