Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Jakadanci Na Kasashen Yammaci Da 'Yan Jarida Sun Bayyana Mamaki Game Da Zaben Kasar Chadi...


'Yan kallon na Afirka sun ce an gudanar da zaben shugaban kasa na Chadi ba tare da ha'inci ba, yayin da hukumar zabe ta kasar Chadi ta bayar da sanarwar cewa wadanda suka jefa kuri'a sun zarce kashi saba'in daga cikin dari.

Kafofin labarai sun bayar da rahoton cewa jami'an jakadanci na kasashen yammaci da kuma 'yan jarida sun bayyana matukar mamakin wannan sanarwa.

An yi wannan zaben ne a tsakanin shugaba Idris Deby da wasu abokansa su hudu. Jam'iyyun hamayya na Chadi sun kauracewa zaben, suka kuma yi kira ga masu jefa kuri'a da su yi zamansu a gida ranar zabe.

A ranar da aka yi zaben, rahotanni sun nuna cewa mutane masu yawa sun yi na'am da kiran kauracewa zaben. Wani wakilin Muryar Amurka ya aiko da rahoton cewa titunan N'Djamena, babban birnin kasar, wayam a ranar zabe, kuma babu alamar ko mai jefa kuri'a guda a rumfunan zabe duk tsawon ranar.

Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka da wasu kungiyoyi goma sha tara masu zaman kansu sun sanya idanu kan wannan zabe na wannan makon.

Ana sa ran hukumar zabe ta Chadi za ta bayar da sanarwatr sakamakon zaben a ranar 14 ga watan Mayu.

XS
SM
MD
LG