Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tawaye Mafi Girma A Darfur Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Cimma Zaman Lafiya Da Gwamnatin Sudan


Kungiyar tawaye mafi girma a yankin Darfur na kasar Sudan ta rattaba hannu kan yarjejeniyar cimma zaman lafiya da gwamnati.

A yau jumma'a ne gwamnatin Sudan da wani bangaren kungiyar 'yan tawaye ta "Sudan Liberation Army" dake karkashin jagorancin Minni Minawi, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a Abuja, babban birnin Nijeriya.

A lokacin da yake magana a wurin bukin sanya hannun, shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya ce yarjejeniyar zata zamo takardar banza kawai idan har sassan ba su doshi aiwatar da ita da aniya mai kyau ba.

Wasu kungiyoyin biyu na 'yan tawaye, watau kungiyar "Justice and Equality Movement" da kuma wani bangaren kungiyar "Sudan Liberation Army" dake karkashin jagorancin Waheed al-Nur, sun ki yarda da wannan kundin zaman lafiya.

Yau jumma'a a nan Washington kuma, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya bayyana fatar cewa dukkan kungiyoyin tawaye za su rungumi wannan yarjejeniya cikin 'yan kwanaki kalilan dake tafe.

Wani dan rajin kare hakkin mutanen Darfur wanda ya jima yana shiga cikin tattaunawar a baya, Abdelbaqi Jibril, ya fadawa Muryar Amurka cewa bai ji dadin gaggawar da aka yi ba, ya kamata masu shiga tsakani su kara lokaci wajen tsara yarjejeniyar da dukkan kungiyoyin tawaye zasu yarda da ita.

XS
SM
MD
LG