Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Mahmoud Ahmadinejad Na Iran Ya Rubutawa Shugaba Bush Wasika


Gwamnatin Iran ta ce shugaba Mahmoud Ahmadinejad ya aikewa da shugaba Bush wata wasika yana bayar da shawarar abinda ta kira sabbin hanyoyin warware tankiyar dake tsakanin Iran da Amurka.

Wani kakakin gwamnati a birnin Teheran, Gholam Hossein Ilham, ya ce shugaban na Iran, "...ya bayar da shawarar sabbin hanyoyin kawar da duniya daga mummunan halin da ta shiga." Bai bayar da karin bayani ba, haka kuma bai fito a fili ya ambaci rikicin da ake yi a kan shirin nukiliya na kasar Iran ba.

A nan Washington, mai bai wa shugaban Amurka shawara a kan harkokin tsaron kasa, Stephen Hadley, ya fada litinin da sanyin safiya cewar ba ya da masaniyar wata wasikar da suka samu daga shugaban Iran. Mr. Hadley ya sake nanata matsayin Amurka cewa ya kamata Iran ta kawo karshen aikin tace karfen Uranium, ya kuma ce gwamnatin shugaba Bush za ta ci gaba da yin aiki tare da kawayenta domin tabbatar da cewa hakan ya faru.

Hukumomi a Teheran sun ce an aike da wasikar ta shugaba Ahmadinejad ne ta hannun ofishin jakadancin kasar Switzerland. Wannan shine karon farko cikin shekaru 26 da aka san shugaban daya daga cikin kasashen biyu ya tuntubi dayan.

Amurka da Iran sun tsinke huldar jakadanci a bayan da wasu dalibai ’yan ta kife an Iran suka mamaye ofishin jakadancin Amurka dake Teheran a watan Nuwambar 1979, inda suka yi garkuwa da Amurkawa na tsawon shekara guda da watanni. Amurka tana neman Kwamitin Sulhun MDD da ya ladabtar da Iran a saboda kin bin umurnin majalisar na dakatar ad aikin tace karfen Uranium.

XS
SM
MD
LG