Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jacob Zuma Ya Ce Zai Koma Ga Harkar Siyasarsa Gadan-Gadan A Jam'iyyarsu Ta ANC


Tsohon mataimakin shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya ce a shirye yake ya koma ga harkokin siyasarsa a jam'iyyarsu ta ANC, kwana guda a bayan da kotu ta wanke shi daga tuhumar yin fyade.

A cikin hirar da yayi da gidan rediyon Afirka ta Kudu, Zuma ya ce da ya ke shari'ar ta kare zai sake hayewa kan kujerarsa a cikin jam'iyyar ANC.

Har ila yau, Mr. Zuma mai shekaru sittin da hudu da haihuwa, ya nemi gafara a saboda bai yi amfani da kororon roba ba lokacin da yayi lalata da macen da ta zarge shi da yi mata fyade, wadda take dauke da cutar kanjamau. Zuma shine tsohon shugaban hukumar yaki da cutar kanjamau a Afirka ta Kudu, kuma ya sha suka mai yawa a lokacin da ya ce yayi wanka bayan jima'i da matar domin wanke duk kwayoyin cutar da watakila suka makale a jikinsa.

Masu fashin bakin siyasa suka ce watakila Mr. Zuma zai nemi kujerar shugabancin Afirka ta Kudu a lokacin zabe na gaba da za a yi a shekarar 2009. Amma kuma shari'ar fyaden da aka yi masa ta zabtare yawan magoya bayansa a cikin jam'iyyar ANC, kuma har yanzu yana fuskantar shari'a kan zarmiya da cin hanci a watan Yuli.

XS
SM
MD
LG