Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Zata kafa cibiyar harkar ciniki a Ikkon Nigeria


Gwamnatin kasar Sin ta bayar da sanarwar cewa zata kirkiro da wani yankin walwalar cinikayya a Lagos, cibiyar kasuwanci ta Nijeriya. Kafofin labarai na kasar Sin sun ce kasar tana shirin zuba jarin dala miliyan dari biyu da sittin da bakwai a kashin farko na bunkasa wannan yankin walwalar cinikayya da ake kira Lekki Free Trade Zone. Shugaban wata tawagar kasar sin dake ziyara a Nijeriya, Chen Xiaoxing, ya ce za a yi amfani da kudin wajen kafa injunan samar da wutar lantarki da gina hanyoyi da masana'antu. Ba a bayyana sauran ka'idojin dake cikin yarjejeniyar ba.

Har ila yau ya bayar da sanarwar cewa kasar Sin zata bai wa Nijeriya rance mai rangwame na dala miliyan dubu biyu da dari biyar, domin kasar ta bunkasa wasu kayayyakin kyautata rayuwar jama'a. Gwamnatin kasar Sin ta ce wannan yankin walwalar cinikayya, wanda zai ringa samar da kayayyaki cikin rahusa sosai, shine irinsa na farko da kasar ta taba kafawa a wata kasar waje. Ta ce tana sa ran samar da aikin yi ga mutane dubu uku tare da bai wa Nijeriya sukunin fita da kayayyakin da za a sarrafa a yankin zuwa kasuwanni a kasashen Turai da Amurka.

XS
SM
MD
LG