Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar kula da makamashi ta kasa da kasa IAEA ta sake kira ga Iran


Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta duniya Mohammed Elbaradei, ya sake nanata kiransa na warware rikicin shirin Nukiliyar kasar Iran ta hanyar diflomasiyya.

Da yake Magana yau Alhamis a Amsterdam, Mohammed El-Baradei yayi marhabin da ganin Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya jinkirta muhawara a kan batun azawa Iran takunkumi. Gwamnatocin kasashen yammacin duniya suna neman kudurin kwamitin sulhu da zai tilastawa Iran ta tsaida tace karfen Uranium ko kuma ta fuskanci takunkumi.

Elbaradei yace yana fatar sassan biyu zasu daidaita a kan matsayi na sassauci da zai tabbatar da bai wa kasar Iran hakkinta na habaka fasahar Nukiliya domin aikin farar hula. Ya kirayi Iran da ita kuma ta soma daukan matakai na kwantarwa da sauran kasashen duniya hankali.

A halin yanzu kuma shugaban kasar ta Iran, Mahmoud Ahmadinejad yace a shirye yake ya tattauna da kowa domin warware rikicin. Da yake Magana yau a kasar Indonesiya, shugaba Ahmadinejad yace abin ban dariya ne kasashen da suka mallaki makaman Nukiliya sune kuma suke matsawa Iran lamba kan nata shirin wanda amfaninsa shine samarda makamashi ba makami ba.XS
SM
MD
LG