Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan Mutane Sun Mutu A Nijeriya


'Yan sanda a Nijeriya sun ce mutane har dari biyu ne suka mutu a lokacin da wani bututun mai yayi bindiga a kusa da birnin Ikko, cibiyar kasuwanci ta kasar.

Hukumomi sun ce fashewar bututun man a yau jumma'a hatsari ne. Suka ce sun yi imani 'yan zaman kashe wando su na kokarin satar mai daga wannan bututun ne sai wani tartsatsi ya haddasa tashin wuta da fashewar. Suka ce cikin dan kankanin lokaci wuta ta lankwame garewanin mai fiye da dari biyar dake wurin.

Wani jami'in Kungiyar Agaji ta Red Cross a Nijeriya ya ce gawarwakin mutane sun kone kurmus ba a iya gane su a inda wannan hatsari ya faru a kauyen Ilado dake bakin ruwa. Ya kara da cewa ba a samu ko da mutum guda da ya kubuta da ransa ba.

Hotunan bidiyo da aka dauka a wurin sun nuna kasussuwan mutane da konannun gawarwaki warwatse a bakin gabar teku a kauyen.

Wani dan jarida dake zaunea birnin Ikko ya fadawa Muryar Amurka cewa mutane sun saba tsiyayewa ko satar mai daga bututun da ya fashe ko wadanda suka fasa da gangan.

XS
SM
MD
LG