Amurka ta kafa takunkumin hana sayarwa da kasar Venezuela makamai a saboda abinda jami'an Amurka suka bayyana a zaman rashin samun goyon bayan kasar ga ayyukan yaki da ta'addanci.
A yau litinin wata mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta zargi hukumomi a birnin Caracas da laifin kasa hana 'yan tawayen kasar Colombia masu ra'ayin gurguzu yin amfani da yankunan kasar Venezuela. Venezuela ta sha musanta cewa tana kyale mayakan Colombia su na yin amfani da kasarta.
Da alamun wannan takunkumin zai kara sukurkuta dangantaka a tsakanin Amurka da Venezuela.
Shugaba Hugo Chavez na Venezuela ya sha sukar yakin da Amurka ta jagoranci kaiwa a kan kasar Iraqi, ya kuma soki Amurka da laifin kulla kai harin soja a kan Iran. A lokacin da yake magana yau litinin a London, shugaban na Venezuela yayi kira ga kasashen duniya, musamman na Turai, da su hana daukar matakan soja a kan Iran a saboda shirinta na nukiliya.