Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Maido Da Huldar Jakadanci Da Kasar Libya


Amurka ta yanke shawarar maido da huldar jakadanci da kasar Libya, tana kuma shirin cire sunan kasar daga cikin jerin kasashe masu goyon bayan ta'addanci.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Condoleeza Rice, ta fada a cikin wata sanarwa cewa an dauki wadannan matakan ne a saboda Libya ta yi tur da ta'addanci ta tsame hannunta daga ciki, ta kuma yanke shawarar yin watsi da makaman nukiliya.

Babban jami'i mai kula da ayyukan yaki da ta'addanci a ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Henry Crumpton, ya ce Libya tana bayar da gudumawa ga tsaron Amurka.

Amma mataimakin sakataren harkokin waje mai kula da al'amuran gabas ta tsakiya, David Welch, ya ce har yanzu Amurka tana da damuwa game da take hakkin bil Adama a Libya, da kuma batun ma'aikatan jinya biyar 'yan kasar Bulgariya da wani likita Bafalasdine da aka yankewa hukumcin kisa bisa zargin sanyawa yara kanana kwayoyin cutar HIV mai janyo kanjamau da gangan.

Amurka ta shafe shekaru fiye da 25 ba ta da huldar jakadanci da kasar Libya.

Ma'aikatar harkokin wajen Libya ta yi marhabin da sanarwar ta yau litinin.

XS
SM
MD
LG