Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce ya yi na'am da shawarar


Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce ya yi na'am da shawarar majalisar dattijai ta kin amincewa da tazarce. A jawabi da yayiwa Jam'iyyar PDP mai mulkin kasar yau alhamis a Abuja, shugaba Obasanjo ya gaya musu cewa su amince da shawarar wakilan majalisa, yanzu su soma shirin zabe mai zuwa. Ranar talata data shige ne Majalisar Dattijai ta yi fatali da kudurin gyara ga kundin tsarin mulki da zai soke wa'adi 2 ga ofishin shugaban kasa a Najeriya. Shi dai Shugaba Obasanjo bai taba fitowa fili yace zai sake tsayawa zabe cikin shekara mai zuwa ba. Amma magoya bayansa sunyi zazzafar kamfain na neman yin gyara ga kundin tsarin mulkin, inda masu adawa da shirin suka zarge su da kokarin sayen 'yan majalisa ta hanyar ba su cin hanci. Jami'an gwamnati sun musanta wannan zargi.
XS
SM
MD
LG