Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Koffi Annan ya damu kwarai saboda kasa warware takaddamar Nukiliyar Iran...


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya bayyana kosawa kan rashin samun ci gaba a kokarin warware rikicin da ake yi da kasashen Iran da Koriya ta Arewa kan shirye-shiryensu na nukiliya. Mr. Annan ya bayyana rikice-rikicen a zaman wadanda suka kazance, yana kuma fadin cewa warware su batu ne na gaggawa.

A cikin jawabin da yayi a Jami'ar Tokyo da kuma a wurin taron manema labarai daga baya, Mr. Annan ya ce akwai bukata ga kasar Iran da ta tattauna ido na ganin ido da kasashen duniya, ita kuma Koriya ta Arewa tilas ne ta komo ga taron kasashe 6 da ya cije, yana mai bayyana wadannan matakan a zaman hanyoyi kadai da ake da su na samun ci gaba. Japan da Amurka da Koriya ta Kudu da Sin da kuma Rasha sun yi kira ga Koriya ta Arewa da ta watsar da makaman nukiliyar da ta ce ta riga ta mallaka. Iran ta nace kan cewa ita shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne, amma kuma Amurka da Tarayyar Turai su na zargin cewa a bayan samar da wutar lantarki, Iran tana da aniyar kera makaman nukiliya.

A jiya laraba, shugaba Mahmoud Ahmadinejad na Iran yayi fatali da shawarar da Tarayyar Turai ta gabatar a baya bayan nan domin warware wannan rikici. Duk da kiyawar da Iran ta sha yi kan amincewa da shawarwarin da ake gabatar mata, Mr. Annan ya ce babu wani shirin zartas da kuduri a gaban Kwamitin Sulhun MDD cikin 'yan kwanakin nan.

XS
SM
MD
LG