Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Sin Ta Bai Wa Nijeriya Agajin Dala Miliyan Dubu Daya


Gwamnatin kasar Sin za ta bai wa Nijeriya kyautar dala miliyan dubu daya domin inganta safarar jiragen kasa.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya bayar da rahoton cewa ministar harkokin kudi ta Nijeriya, Ngozi Okonja-Iwuala, ita ce ta bayar da sanarwar wannan agaji ranar lahadi a lokacin wani taron agaji na kasa da kasa a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Ministar ta ce za a yi amfani da wannan kudin domin shimfida sabbin layukan dogo tare da gyara wadanda suka lalace.

A wani gefen kuma, kamfanin samar da wutar lantarki mallakar gwamnatin Nijeriya ya ce ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar dala miliyan 110 da wani kamfanin kasar Sin domin kara tsawon wani layin dake dauke da lantarki.

Kasar Sin ta kara kaimin zuba jari a Nijeriya a yayin da take kokarin neman sabbin kasuwanni ga kayayyakinta, da kuma hanyoyin samun mai. A makon da ya shige, Nijeriya ta bai wa kasar Sin sabbin lasisi guda hudu na tonon mai, yayin da Sin ta yi alkawarin zuba jarin dala miliyan dubu biyu a wata matatar man fetur.

XS
SM
MD
LG