Ma'aikatan kiwon lafiya a tsibirin Java wanda girgizar kasa ta yi wa kaca-kaca a kasar Indonesiya sun ce su na ci gaba da gwagwarmayar jinyar dubban mutanen da suka ji rauni, yayin da wasu dubban suke ci gaba da kwarara zuwa asibitocin da tuni suka cika har suka batse. A yanzu likitoci su na gudanar da kananan ayyukan tiyata a sararin subhana.
A lardin Yogyakarta inda girgizar ta fi shafa, inda kuma da yawa daga cikin mutane kimanin dubu biyar suka rasa rayukansu, ma'aikatan agaji sun ce sun fara karancin abinci, da ruwan sha da magunguna.
Jami'an kasar Indonesiya sun yi kiyasin cewa mutane kusan dubu metan sun rasa gidajensu a girgizar kasa mai karfin awu 6 da digo uku a ma'aunin motsin kasa na Richter, wadda aka yi a yankin ranar asabar. An ce da yawa daga cikin mutanen yanzu sun jeru a kan titunan birnin Yogyakarta su na barar abinci da kayan masarufi.
Kayayyakin agaji daga kasashen waje sun fara shiga yankin, inda kungiyoyin agaji suka kai wasu kayayyakin a cikin motocin jigilar kayayyaki. Shugaba Susilo Bambang Yudhoyono ya kafa sansani a birnin Yogyakarta, yana sanya idanu kan ayyukan agajin da kansa. Ya roki kasashen waje da su agaza musu, ya kuma yi alkawarin samar da dala miliyan dari da bakwai domin gudanar da ayyukan sake gina yankin.