Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sashen Hausa Na Muryar Amurka Zai Yi Ban Kwana Da Dadaddiyar Fardusa, Donnie Butler


A bayan da ta shafe shekaru talatin da bakwai tana aiki, dadaddiyar Fardusar Sashen Hausa na Muryar Amurka ta yanke shawarar za ta yi ritaya.

Donnie Virginia Butler, wadda ta fara aikin gwamnati tun cikin watan Yunin shekarar 1969, ta zamo Fardusa a Sashen hausa na Muryar Amurka tun cikin shekarar 1984.

A ranar alhamisar nan sashen Afirka zai gudanar da wata kasaitacciyar liyafar ban kwana da Donnie Butler. A ranar Jumma'a kuma, Sashen Hausa zai gudanar da ta sa liyafar ta cin abincin rana domin ban kwana da wannan baiwar Allah wadda kowa cikin Sashen zai yi kewarta.

A lokacin da take tattaunawa da filin "A Bari Ya Huce...", Mrs. Butler ta ce ma'aikatan sashen Hausa sun wuce matsayin abokan aikinta, sun zamo 'yan'uwanta, domin ba zata taba mantawa da wannan sashe ba, ko kuma dimbin masu sauraron sashen Hausa.

Donnie Butler ta ce Allah ne Ya kaddara zuwanta Sashen Hausa, kuma ta ji dadin hakan. Ta ce a yanzu ma, nufin Allah ne za ta rungumi wani sabon abu, musamman a daidai wannan lokaci a rayuwarta.

Masu sauraronmu su na iya aikowa da sakonninsu na ban kwana wadanda zamu hada cikin shirin ban kwana na musamman da zamu gabatar ranar asabar da safe a filin "A Bari Ya Huce...", kuma zamu buga kofe domin bayarwa ga ita Donnie Butler a zaman tsarabar masu sauraro.

XS
SM
MD
LG